An sauke ministar da za ta sayi alawar miliyoyin dala a Madagascar

An sauke ministar Ilimin Madagascar bayan an gano cewa ta yi shirin sayen alawa mai tsinke ta dala miliyan 2.2.
A makon jiya Rijasoa Andriamanana ta ce ta bayar da umarnin sayo alawar ga kananan yara don ba su ita tare da maganin korona don kashe kaifin dacin maganin, a cewar kamfanin dillacin labarai na AFP.
Maganin gargajiyar na Covid-Organics shi ne ganyen da gwamnatin kasar ta rika tallatawa wasu kasashe inda ta ce yana maganin Covid-19.
Ko da yake Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce babu wani riga-kafi ko magani cutar korona kawo yanzu.
AFP ya ce ana sa ran kowanne dalibi a kasar zai samu alawa uku.
Kafofin watsa labaran kasar sun ce ministar ta fasa shirin sayo alwarar bayan Shugaba Andry Rajoelina ya ki amincewa da bukatarta.
Ranar Alhamis aka sanar da korar ministar a wata sanarwa da inda aka ce takwararta a ma'aikatar ilimi mai zurfi , Elia Béatrice Assoumacou, za ta maye gurbinta don yin rikon-kwarya.
Comments
Post a Comment