Skip to main content

Wanne abinci ya kamata mu rinka ci?

Wanne abinci ya kamata mu rinka ci?
Yayin da ake samun karin shawarwari masu karo da juna game da abinci mai rai da lafiya, me ya kamata mu rika ci domin mu zauna lafiya?
Gwamnatin Burtaniya a baya-bayan nan ta sake nazarin shawarwarinta kan irin abincin da yake gina jiki ta hanyar kallon hujjar da ke a bayyane.
Littafin da ke bayanin irin abincin da ya kamata mu rika ci na Eatwell Guide ya jero manyan rukunnan abinci guda biyar da ya kamata a ce muna ci, da kuma abubuwan da za mu takaita ci ko kuma kaucewa ci.

Kitse/Maiko
Kitse yana da muhimmanci a cikin abincinmu. Muna bukatar mu ci kitse domin mu zauna lafiya. Amma kuma kada mu rinka ci da yawa.
A littafin abinci na Eatwell Guide, kitse ya kunshi mai da kuma man shanu.
Ana daukar man zaitun da man girki a matsayin wadanda suka fi lafiya fiye da man alade da kuma man shanu. Amma ba kowa ba ne ya amince da haka.
Wasu na ganin cewa gwanda man shanu. Amma ka tabbatar cewa ba ka ci da yawa ba.
Madara
Madara da cuku da kindirmo a wasu lokuta na dauke da kitse- amma su ma ana samun abubuwan dake gina jiki da kuma wasu bitamin har ma da alli a cikinsu. Allin na da kyau ga kasusuwanmu. A cikin littafin irin abincin da ya kamata mu rika ci na Eatwell guide, sun kunshi kusan kashi shida na abincin da ya kamata mu ci
Akan iya lafta sukari kan wasu nau'in abincin masu dauke da madara a cikinsu, koma da ace suna kunshe ne da kitsen da bai ka kawo ba
Kamata ya yi dai ka rinka cin abincin da babu kitse da kuma sukari sosai a cikinsu kamar tsurar kindirmo
Abinci mai kara kuzari
Wannan wani na'uin abinci ne da ake takaddama akansa tsakanin masu bayar da shawarar irin abincin da mutum zai ci.
Hakkin mallakar hotoSCIENCE PHOTO LIBRARY
Wasu na cewa an mayar da hankali sosai a kan abinci kamar biredi da dankali, kuma cin su da yawa ka iya janyo karuwar hadarin kamuwa da cutar suga.
Gwamnati ta ce irin wadannan nau'ikan abinci suna da kyau wajen samun karfin jiki, kuma kamata ya yi abincin da muke ci ya kasance yana dauke ne da sama da kashi uku na wannan nau'in abincin.
Kayan itace da kuma ganye
Wannan shi ne nau'in abincin da ya kamata a ce muna ci - duk da haka da yawa daga cikinmu ba sa cin wadataccen 'ya'yan itatuwa da kuma ganye.
Hakkin mallakar hotoSCIENCE PHOTO LIBRARY
Kamata ya yi su kunshi kashi uku na abincin da muke ci a kulli yaumin saboda suna dauke da bitamin da abinci mai harza da kuma Minerals.
Sai dai ka yi hankali da lemukan gwangwani na 'ya'yan itatuwa saboda suna iya dauke da suga da yawa a cikinsu. Shi ya sa ya kamata ka takaita shan irin lemukan 'ya'yan itatuwa zuwa abin da bai wuce 150ml a rana ba.
Abinci mai gina jiki
Nama shi ne abin da ya fi, amma kifi da wake da kwai da gyada su ma ana samun sinadaran gina jiki a cikinsu.
Hakkin mallakar hotoSCIENCE PHOTO LIBRARY
Sai dai ka sake tunanin wasu abubuwan kuma da ke ciki wannan nau'in abinci. Nama ka iya kasancewa yana dauke da kitse. Haka kuma ana iya samu wani nau'in suga cikin wani waken gwangwanin.
Kodayake kifin sardines da na salmon yana da kyau ga lafiyarmu amma kada mu ci fiye da kima a cikin mako guda.
Abincin da za a kauracewa
Abinci da a zahiri yake barazana ga lafiyarmu da kuma wanda za a takaita ci ko ma a daina ci su ne irinsu kek da cakulan da lemukan da ke dauke da suga.
Hakkin mallakar hotoSPL
Akwai abinci da yawa da ke kunshe da gishiri da yawa da kitse da suga amma ba nan take mai cinsu yake kula ba.
Abin da za ka sha
Kamata ya yi manya su sha kusan kofi takwas na ruwa a kowacce rana. Shayi da kuma kofi ka iya kasancewa ciki.
Haka ma lemon dan itace shi ma ya kan iya zama ruwa amma kada ka sha fiye da kofi daya saboda yana dauke da suga.
Barasa ba ta cikin littafin abinci na Eatwell Guide. Tana dauke da suga sosai.

Comments

Popular posts from this blog

Rayuwar karya yazama ruwan dare ashafin instagram

Matasan zamani na anfani da shapin domin yima yan mata karya<chilling> don nuna rayuwar karya wato ta kafan social media da anfanin  da wanan shapi  don yada munufa na karya kadaan daga cikin wanda suka fi sha hara a wannan karyan sune 1-Bilalgy"bilal ado gaya"  Mezama a garin kano hottoro tsamiyar boka

An sauke ministar da za ta sayi alawar miliyoyin dala a Madagascar

An sauke ministar da za ta sayi alawar miliyoyin dala a Madagascar 6 Yuni 2020 Aika wannan shafi Facebook   Aika wannan shafi Messenger   Aika wannan shafi Twitter   Aika wannan shafi Email   Aika Hakkin mallakar hoto MIXITISTOCK An sauke ministar Ilimin Madagascar bayan an gano cewa ta yi shirin sayen alawa mai tsinke ta dala miliyan 2.2. A makon jiya Rijasoa Andriamanana ta ce ta bayar da umarnin sayo alawar ga kananan yara don ba su ita tare da maganin korona don kashe kaifin dacin maganin, a cewar kamfanin dillacin labarai na AFP. Maganin gargajiyar na Covid-Organics shi ne ganyen da gwamnatin kasar ta rika tallatawa wasu kasashe inda ta ce yana maganin Covid-19. Ko da yake Hukumar Lafiya ta Duniya  ta ce babu wani riga-kafi ko magani cutar korona kawo yanzu. AFP ya ce ana sa ran kowanne dalibi a kasar zai samu alawa uku. Kafofin watsa labaran kasar sun ce ministar ta fasa shirin sayo alwarar bayan Shugaba Andry Rajoel...

Shin kokasan rashin shan ruwa yakan ja idon mutum ya bushe

                                  Shin kokasan rashin shan ruwa yakan ja idon mutum ya bushe Shin kokasan rashin shan ruwa yakan ja idon mutum ya bushe? Domin kauracewa hakan kurika shan ruwa akai akai sannan kuyi anfani da eye drops wanda likitanku ya rubuta maku. daga   O.D yasir Isa MAgaji