Wanne abinci ya kamata mu rinka ci? Yayin da ake samun karin shawarwari masu karo da juna game da abinci mai rai da lafiya, me ya kamata mu rika ci domin mu zauna lafiya? Gwamnatin Burtaniya a baya-bayan nan ta sake nazarin shawarwarinta kan irin abincin da yake gina jiki ta hanyar kallon hujjar da ke a bayyane. Littafin da ke bayanin irin abincin da ya kamata mu rika ci na Eatwell Guide ya jero manyan rukunnan abinci guda biyar da ya kamata a ce muna ci, da kuma abubuwan da za mu takaita ci ko kuma kaucewa ci. Kitse/Maiko Kitse yana da muhimmanci a cikin abincinmu. Muna bukatar mu ci kitse domin mu zauna lafiya. Amma kuma kada mu rinka ci da yawa. A littafin abinci na Eatwell Guide, kitse ya kunshi mai da kuma man shanu. Ana daukar man zaitun da man girki a matsayin wadanda suka fi lafiya fiye da man alade da kuma man shanu. Amma ba kowa ba ne ya amince da haka. Wasu na ganin cewa gwanda man shanu. Amma ka tabbatar cewa ba ka ci da yawa ba. Madara Madara da cu...


Comments
Post a Comment