Yawan masu cutar korona a Najeriya ya kai wani gagarumin mataki, inda ya haura mutum 11,000. Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta ƙasar ta nuna cikin alƙaluman da fitar cewa an gano ƙarin mutum 348 ranar Laraba da suka sake kamuwa da ƙwayar cutar. A yau ma Legas, jihar da annobar ta fi tsanani a Najeriya, an sake samun mutum 163 da suka kamu. Abuja kuma, babban birnin Najeriya, mutum 76 ne aka ba da rahoton cutar ta sake shafa. Haka zalika, alƙaluman NCDC sun nuna cewa an kara samun wadanda suka rasu sakamakon cutar inda yanzu adadinsu ya kai 315. Sai dai kuma, an kara samun wadanda suka warke abin da a yanzu adadinsu ya kai 3,329. Jihar Ebonyi ita tazo ta uku a yawan wadanda suka kamu da cutar a ranar Laraba inda ta ke da mutum 23, sai Rivers 21, sai Delta inda aka gano mutum 8, Nasarawa ma 8 da kuma Neja ma 8. Enugu na da mutum 6, Bauchi da Edo da Ekiti da Ondo da kuma Gombe nada mutum biyar-biyar, sai Benue 4, Ogun 2, Osun da Plateau da Kogi da kuma Anambra nada mu...